Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Aiwatar Da Yarjejeniyar Tsaro Tsakanin Iran Da Iraki

Shugaban kasar Iran ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen Iran da Iraki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada wajabcin aiwatar da

Shugaban kasar Iran ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen Iran da Iraki

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyoyin tsaro da aka kulla tsakanin kasashen Iran da Iraki, wadanda zasu kai ga karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a fagen yaki da ta’addanci da tunkarar makiya.

Shugaba Pezashkian ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da fira ministan kasar Iraki Muhammad Shiya’a Al-Sudani a babban birnin kasar Iraki Bagadaza a jiya Laraba: Yana mai jaddada cewa sun gudanar da tattaunawa mai muhimmancin matuka da fira ministan Iraki kuma ta kasance babbar dama ta ziyararsa a kasar da take abokiya kuma ‘yar uwa, a ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan dare karagar shugabancin Iran.

Shugaban na Iran ya kuma bayyana cewa: Sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 14 a tsakanin Iran da Iraki, wanda hakan ya zama mafarin fadada alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments