Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Ta Amnesty Int’l Ta Bukaci Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Saki Shugaban Kungiyar Kwadagon Kasar  Da Aka Kama

Kungiyar kwadago a tarayyar Najeriya tare da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty Int’l sun fidda sanarwa daban daban ta bukatar gwamnatin shugaba Bola Ahmed

Kungiyar kwadago a tarayyar Najeriya tare da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty Int’l  sun fidda sanarwa daban daban ta bukatar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta saki shugaban kungiyar kwadago Mr  Joe Ajaero wanda jami’an tsaro na DSS suka yi a safiyar yau litinin.

Jaridar Premium times ta bayyana cewa a safiyar yau Litinin ce jami’an hukumar DSS suka kama Mr Ajaero a lokacinda yake kokarin shiga jirgi zuwa birnin London don halattar wani taro dangane da ma’aikata.

Kungiyar ta kara da cewa gwamnatin shugaba Tinubu tana kara lalacewa da kama masu fafutuka don kyautata rayuwar ma’aikata a kasar.

Isa Sanusi shugaban kungiyar Amnesty International a Najeriya a wani rubutu da yayi a kafafen sada zumunta ya bayyana takaicinsa da yadda gwamnatin shugaba Tinubu take takurawa shuwagabannin kungiyar ma’aikata NLC saboda gwagwarmaya da suke yi don cimma manufa ta kyautatawa ma’aikata a tarayyar Najeriya, musamman bayan kara farashin makamashin da gwamnatin tarayya ta yi a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments