Rikici Yana Kara Tsananta Tsakanin Firayi Minista Da Minista Yakin Isra’ila

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya bayar da rahoton cewa,  Kafafen yada labaran Amurka sun bayyana cewa, rikicin da ke tsakanin Firaministan da Ministan yakin gwamnatin

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya bayar da rahoton cewa,  Kafafen yada labaran Amurka sun bayyana cewa, rikicin da ke tsakanin Firaministan da Ministan yakin gwamnatin Sahayoniya kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza yana ci gaba da kara tsananta.

An gudanar da taron majalisar ministocin gwamnatin sahyoniyawa dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, inda shafin sadarwa na yanar gizo na Axios ya bayar da rahoton cewa, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gabatar da taswirar yankin Saladin ko kuma (Philadelphia) a wannan taro, da nufin dora mahangarsa kan cewa sojojin Isra’ila su ci gaba da kasancewa a wannan wuri, wanda yake kan iyakan Gaza da kasar Masar, amma Yav Galant “Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya caccake shi kan hakan, tare da zargin Netanyahu da shiga cikin aikin da ba nasa ba, ta hanyar yi wa sojojin Isra’ila tsare-tsare abin da zasu aiwatar a wajen yakin.

Ministan yakin gwamnatin sahyoniyawan Yoav Gallant, ya ce kamata ya yi majalisar ministocin kasar ta nemi tsagaita bude wuta da wuri, kuma ya kamata a a fadada wannan yarjejeniya ta yadda ba za ta takaita da batun musayar fursunoni ba kawai, domin kuwa Isra’ilawa da dama suna daukar batun yarjejeniyar da matukar muhimamnci, inji Yoav Gallant.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments