Shugaba Putin Ya Gana Da Jama'a A Birnin Mariupol

2023-03-19 16:24:16
Shugaba Putin Ya Gana Da Jama'a A Birnin Mariupol

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya kai ziyarar ba zata zuwa birnin Mariupol.

Kakafen yada labaran Rasha sun ruwaito cewa shugaba Putin ya kewaya cikin birnin Mariupol cikin mota tare da zantawa da mazauna yankin.

A karon farko tun bayan matakin sojin da kasar Rasha ta ce ta dauka kan Ukraine, shugaba Vladmir Putin na Rasha ya kai ziyara yankin Donbas dake karkashin ikon dakarunsa.

Tuni Ukraine ta caccaki ziyarar tana mai danganta ta data wani babban mai laifi na kasa da kasa.

Ziyarar na zuwa ne bayan wata da ya kai yankin Crimea a jiya Asabar, kwana guda bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta nemi a cafke mata shi.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!