Rahotanni sun bayyana cewa Papa roma farancis shugaban cocin katolika na duniya ya bada shawarar komawa teburin tattaunawa domin kawo karshen yakin da ake yi a Gaza da kuma kasar Ukrain,
Da yake hira da gidan talabijin din CBS ya fadi cewa kasashen dake cikin yaki a halin yanzu su dakatar da yaki su koma teburin tattaunawa domin yin sulhu , don shi ne yafi dacewa akan cigaba da yaki mara karewa.
Haka zalika ya bukaci a bada damar kai bawa alummar gaza abinci, yace yara kanana suna rayuwa cikin wani hali mafi muni sun manta da yin dariya, daga ranar 7 ga watan oktoban shekarar bara Isra’ila ta kaddamar da hari da kisan kiyashi a Gaza da goyon bayan Amurka, inda ta kashe dubban falasdinawa da mafi yawancinsu mata ne da yara kanana,
Daga karshe ya bayyana cewa hare-haren na Isra’ila a ya koma na Ta’addanci