Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdallahiyan da yake nuna damuwarsa game da yin amfani fiye da karfi da jamian tsaron kasar Amurka ke yi kan malamai da daliban jami’a dake zanga zangar adawa da laifukan yaki da HKI ke tafkwa kan Alummar falasdinu yace dole ne fadar white hause ta dakatar da goyon baya ido rufe da take bawa gwamnatin Isra’ila.
Zanga zangar nuna adawa da ci gaba da kisan kiyashi da HKI ke yi a yankin Gaza ya shiga cikin jami’oin Amurka, inda a jami’ar taxzas kalfoniya ta kudu inda aka yi taho mugama tsakanin jamiyan yan sanda da sauran dalibai, da suke zanga zangar adawar da kisan kare dangi a Gaza
Ministan ya kara da cewa kisan kare dangi kan dubban mata da yara kanana musamman bayan gano wawakeken ramin da aka bizne marasa lafiya da wadanda aka jikkata a kusa da Asibitin Ansar dake zairin gaza ya jawo kyama da nuna kin jinin gwamnatin yahudawan sahyuniya da baya boyuwa a kasashen duniya.