Search
Close this search box.

Iran Ba Zata Mika Kai Ga Manufofin Amurka Na Nuna Fin Karfi Ba

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminaee ya bayyana cewa mutanen Iran ba zasu taba mika kai ga bukatun

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminaee ya bayyana cewa mutanen Iran ba zasu taba mika kai ga bukatun Amurka da kuma nuna fin karfinta ba.

Kamfanin dillancin labaran Sahab ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Laraba, a lokacinda yake jawabi a gaban wasu ma’aikata a gidansa nan Tehran. Ya kuma kara da cewa mutanen kasar Iran zasu maida takunkuman tattalin arzikin da Amurka da kawayenta suka dorawa kasar a matsayin dama na samar da ci gaba a kasar.

Jagoran ya kara da cewa, ayyukan ci gaba wadanda ma’aikata a cikin kasar suka yi a kasar zasu taimaka wajen kyautata tattalin arzikin kasar. Sannan tare da ci gaban da ake samu takunkuman kasashen Amurka da kawayenta ba zasu yi wani tasiri ba, banda haka wannan zai maida Iran kasa mai cikekken yenci wacce kuma take girma take kuma samun ci gaba.

A wani bangare na jawabinsa Jagoran ya ce kasashen yamma musamman Amurka sun dorawa kasar mummunan takunkuman tattalin arziki ne, da sunan taake hakkin bil’adama da kuma da kuma shirinta na makamashin nukliya, amma duk da wannan basa daukar HKI a matsayin kasa mai take hakkin biladama. Duk tare da kisan kare dangane da take yiwa al-ummar gaza, tun cikin watan octoban da ya gabata.

Daga karshe ya bayyana cewa kera makamai a cikin gida wanda JMI take yi yana daga cikin maida takunkuman tattalin arziki zuwa dama. Wannan kuma ya bawa masana da dama mamaki kan yadda Iran ta sami irin wannan ci gaban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments