Rahotanni sun bayyana cewa Fira ministan Isra’ila Binyamin Natanyaho ya bayyana daliban Jami’a dake zanga-zangar nuna goyan bayan falasdinawa da daliban jami’a ke yi a kasar Amurka a matsayin masu nuna kyamar yahudawa, kuma ya bukaci a kawo karshenta cikin gaggawa.
Nuna rashin amincewa da kafa tantuna a jami’aoi da kuma bukatar kawo karshen hada kai da masu aikewa da isra’ila makamai saboda laifukan yaki da HKI ke tafakwa kan alummar gaza acikin kasa da mako daya ya yadu zuwa sauran jami’oi Amurka
Nuna rashin amincewar da daliban jami’oin Amurka suka gudanar ya jawo kama daruruwan daliban jami’a a birnin Newyork Texas da kuma kalifonia.daga lokacin kaddamar da harin guguwar Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma harin soji da Isra’ila ta kai a gaza Jami’oin Amurka suka koma sansanin gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Isra’ila.