A cikin wani bayani na hadin guiwa da kasashen Pakistan da Iran suka fitar sun bukaci dakatar da bude wuta cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba, kuma a bada damar isar da kayan agaji ga alummar gaza da aka mamaye da bawa yan gudun hijara damar komawa gidajensu.
A karshen ziyarar da shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya kai a kasar Pakistan dukkan bangarorin biyu sun tir da laifukan yaki da Isra’ila ta tafka kan alummar Falasdinu da kuma killacesu da hana shigar da abinci da magunguna da hakan yayi sandiyar mutuwar falasdinawa da dama,
Daga karshe bangarorin biyu sun nuna goyon bayansu ga duk wani matakin adalci mai dorewa da zai warware rikicin, bisa mutunta ra’ayoyin alummar falasdinu, gwamntin Isra’ila bisa goyon bayan Amurka ta yi kisan kiyashi kan alummar Gaza da gabar yammacin kogin Jodan .