Zarif: Iran Ba Zata Daina Taimakawa Mutanen Yemen Da Ake Zalunta Ba

2021-02-24 08:57:01
Zarif: Iran Ba Zata Daina Taimakawa Mutanen Yemen Da Ake Zalunta Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zareef ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa tana goyon bayan duk wani kokarin na kawo karshen yakin fin karfin da ake nunawa mutanen kasar Yemen.

Majiyar muryar JMI ta nakalto shafin labarai na tashar talabijin ta Al-Misirah yana fadar haka a hirar da ta yi da ministan a birnin Tehran. Zareef ya kammala da cewa gwamnatin JMI tana son ganin da farko an dakatar da yaki, sannan a dagewa kasar ta Yemen kofar ragon da aka yi mata, sannan a kai masu agajin gaggawa , wadanda suka hada da abinci da magunguna.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!