​Imam Khamenei: Iran Za Ta Iya Kara Yawan Uranium Da Take Tacewa Daga Kashi 20% Har zuwa 60%

2021-02-22 21:55:39
​Imam Khamenei: Iran Za Ta Iya Kara Yawan Uranium Da Take Tacewa Daga Kashi 20% Har zuwa 60%

Jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran ya bayyana cewa, Iran za ta iya tace sanadarin uranium daga kashi 20% zuwa kashi 60% matukar dai tana da bukatar yin hakan.

Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaba da kuma mabobin majalisar kwararru masu zaben jagora a kasar.

Ya ce kalaman da Amurka da kuma kasashen turai uku, Jamus, Burtaniya gami da Faransa suka yi kan Iran da shirinta na nukiliya, kalamai ne na girman kai da nuna isa, wanda kuma Iran ba za ta amince da hakan.

Dangane da matakan da Iran din take dauka wajen jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar nukiliya kuwa, jagoran ya ce Iran din za ta kasance mai yin aiki da wannan yarjejeniyar matukar sauran bangarori suka yi aiki da ita.

Ya ce kasashen turai sun sani sarai kan cewa shirin na Iran ba n kera makaman nukiliya ba ne, amma suna yin amfani da hakan ne domin kara matsin lamba a kanta domin ta mika wuya., ya ce idan suna bukatar kera makaman nukiliya za su iya yi, amma kuma ba za su yi ba saboda hakan ya sabawa koyarwa irin ta addinin muslunci.

Ya ce aikin tace sanadarin uranium kashi 20% da Iran take yi za ta iya kara shi zuwa kashi 60%, matukar dai akwai bukatar hakan.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!