Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran wanda ya karbi bakuncin shugabansa na duniya, anan Iran ya yaba da yadda aiki a tsakanin bangarorin yake tafiya.
Shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta Iran, Muhammad Salami ya ce; Dukkanin masu bata yadda alaka take a tsakanin Iran da hukumar makamashin Nukiliyar ta duniya, sun ji kunya.
Muhammad Salami ya bayyana hakan ne dai a yayin taron manema labaru na hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa, Rafael Mariano Grossi a birnin Isfahan da ake gabatar da taron karawa juna sani akan Makamashin Nukiliya wanda shi ne irinsa na farko a Iran.
Salami ya bayyana ziyarar Rafael a karkashin yadda bangarorin biyu suke aiki da juna, sannan ya kara da cewa; Iran ba ta fita daga karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya ba, Amurka ce ta fitar da kanta daga ciki.
A nashi gefen, shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya yi ishara da yadda a jiya Litinin ya gana da manyan jami’an Iran idan su ka tattauna hanyoyin aiki tare a tsakaninsu.