Search
Close this search box.

UNICEF: Kananan Yara 600,000 Ba Su Da Mafaka A Yankin Rafah

Asusun kananan yara na MDD, ( UNICEF) ya yi gargadi akan kai wa yankin Rafah da HKI take yi, yana mai cewa da akwai kananan

Asusun kananan yara na MDD, ( UNICEF) ya yi gargadi akan kai wa yankin Rafah da HKI take yi, yana mai cewa da akwai kananan yara da adadinsu ya kai 600,000 wadanda ba su da amintaccen wuri da za su rayu a ciki.

Ita ma hukumar agaji ta MDD, ( UNRWA) ta yi nata gargadin akan rashin shigar da makamashi da sauran kayan agaji zuwa cikin yankin musamman ta mashigar Rafah.

Hukumar ta kuma ce, matukar aka dakatar da shigar da kayan agajin ta wannan hanya, to yunwa za ta tsananta  a yankin na arewacin Gaza.

Kakakin kungiyar agaji ta “Red Crescent” ta Falasdinu ta bayyana cewa; Kai wa yankin Rafah hari zai jera rayuwar dubban Falasdinawa  fararen hula a cikin hatsari,kuma za a sami tabarbarewar harkokin kiwon lafiya.

Kakakin kungiyar ta “Red Crescent” ta Falasdinawa ya kara da cewa babu wani wuri a fadin Gaza, wanda zai iya daukar ‘yan hijira miliyan daya da rabi.

Abinda aka fi zullumi akansa a yanzu shi ne yadda ‘yan sahayoniyar za su hana motocin daukar majiyyata shiga yankin domin taimakawa da daukar wadanda su ka jikkata.

Kididdigar Falasdinawa tana cewa, ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 34,000 da 789,mafi yawancinsu kananan yara ne da mata. Adadin wadnda su ka jikkata kuwa sun kai dubu 78 da 204,su ma mafi yawancinsu mata ne da kananan yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments