Search
Close this search box.

Abdollahian: Haniya Ya Sanar Da Iran Amincewar Hamas Da Shirin Dakatar Da Bude Wuta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya ce, shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya yi masa bayani kan matakin da kungiyar ta dauka kan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya ce, shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya yi masa bayani kan matakin da kungiyar ta dauka kan shirin dakatar da  bude wuta a zirin Gaza.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin, Amir-Abdollahian ya ce, Haniyeh ya yaba da irin gagarumin matsayin da Iran ta dauka, kan batun yakin da Isra’ila take kaddamarwa a kan al’ummar yankin zirin Gaza.

Ministan na Iran ya kara da cewa, Haniyeh ya kuma yi masa bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa a halin yanzu a yankin Gaza da yakin Isra’ila ya daidaita.

Ya jaddada cewa Haniyeh ya ce ya mika martanin Hamas kan shirin hadin gwiwa tsakanin Masar da Qatar na kawo karshen hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa, da musayar fursunonin da kuma kawo karshen killacewar da yahudawa suke yi wa Gaza.

Amir-Abdollahian ya nakalto Haniyeh yana cewa “A yanzu shawara ta rage Isra’ila.”

A takaice dai sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar a jiya litinin ta ce kungiyar ta amince da shawarar dakatar da bude wuta a Gaza, inda take tunkarar hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kai na tsawon watanni bakwai, wanda ya yi sanadin shahadar dubban mutane.

A cewar sanarwar, Haniyeh ya sanar da masu shiga tsakani na Qatar da Masar cewa Hamas ta amince da shawararsu ta tsagaita bude wuta a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments