Search
Close this search box.

Lebanon:  Sojojin HKI 40 Ne Su Ka Halaka Da Jikkata Akan Iyaka Da Lebanon A Watan Afrilu

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a cikin watan Afrilu sojojin HKI da su ka halaka sanadiyyar hare-haren Hizbullah,sun kai 3,yayin da wasu 37

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a cikin watan Afrilu sojojin HKI da su ka halaka sanadiyyar hare-haren Hizbullah,sun kai 3,yayin da wasu 37 su ka jikkata sanadiyyar hare-haren da kungiyar Hizbullah take kai wa.

Rahotannin sun kuma ambaci cewa wasu sojojin mamayar 2 sun halaka sanadiyyar harin da Hizbullah ta kai da jirgin sama maras matuki a ranar Litinin din da ta gabata a yankin “Mutullah’.

Daga cikin muhimman cibiyoyin sojojin HKI da kungiyar Hizbullah ta kai wa hare-hare a cikin watan Afrilu da akwai “arabul-Aramisha’ sai sansanin sojan mamaya na “Avavim” dake yankin Jalil.

Tun bayan da HKI ta shelanta yaki akan Gaza ne dai kungiyar ta Hizbullah ta shiga taya Falasdinawa fada ta hanyar kai wa sansanonin soja da cibiyoyin leken asirin ‘yan mamaya hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments