Sahel : MDD Ta Nemi A Samar Da Kudaden Wanzar Da Zaman Lafiya

2021-02-18 09:33:14
Sahel : MDD Ta Nemi A Samar Da Kudaden Wanzar Da Zaman Lafiya

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci a samar da kudaden da ake hasashen samu don gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel.

A wani sakon bidiyo da ya gabatarwa taron kolin kungiyar kasashen G5 na yankin Sahel wanda ya gudana a birnin N'Djamena, na kasar Chadi, Mista Guterres ya ce, ya kamata shirin wanzar da zaman lafiya da yaki da ayyukan ta’addanci na Afrika ya dinga samun umarni daga kwamitin sulhun MDD da kuma samun kudaden tafiyar da shirin.

Kungiyar G5 Sahel, ta kumshi kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da jamhuriyar Nijer, kuma kungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsanancin yanayin tabarbarewa tsaro da ayyukan jin kan bil adama a shiyyar.


024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!