Rauhani: Dole Ne Biden Ya Janye Takunkumai Kan Iran Kafin Duk Wani Batu Kan Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan
Rauhani ya bayyana cewa, dole ne gwamnatin Joe Biden ta janye dukkanin
takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran, kafin Iran ta koma yin aiki da
bangarorin yarjejeniyar nukiliya da ta jingine.
Shugaba Rauhani ya bayyana haka ne a
wata zantawa da ta gudana tsakaninsa da shugaban kasar Switzerland Guy Parmelin
a daren jiya, inda ya jaddada cewa Iran tana kan bakanta, na cewa dole ne
dukkanin bangarorin da suke cikin yarjejeniyar nukiliya da suka rattaba hannu a
kanta, su yi aiki da ita lokaci guda.
Ya ce siyasar matsin lamba da kakaba
takunkumi a kan Iran da tsohuwar gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Donald
Trump ta dauka, ba ta yi nasara ba, domin hakan bai iya tilasta Iran din ta ja
da baya daga irin matakan da ta dauka ba.
Ya ce kasarsa za ta koma yin aiki da
yarjeneiyar bayan jingine yin aiki da wasu bangarorinta, da zaran Amurka ta
janye takunkuman da ta kakaba mata.
Shi ma a nasa bangaren shugaban
kasar ta Switzerland Guy Parmelin ya bayyana cewa, wajibi ne a kan dukkanin
bangarori su girmama abin da ke cikin yarjejeniyar, ta hanyar yin aiki da abin
da ke cikinta, kamar yadda ya sha alwashin cewa zai tattara kudaden Iran da aka
rike a wasu kasashen duniya, domin mika su ga kasar ta Iran ta hanyoyin da suka
dace.
015