Amurka : An Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Harin Da Aka Kai Wa Majalisa

2021-02-16 09:41:36
Amurka : An Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Harin Da Aka Kai Wa Majalisa

A Amurka an kafa wata hukuma ta musamman da za ta binciki harin da magoya bayan tsohon shugaban kasar suka kai wa ginin majalisar dokokin a ranar 6 ga watan jiya.

Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi, ta ce hukumar da za a kafa za ta binciki ainihin abubuwan da su ka faru dangane da harin da aka kaiwa majalisar.

Wannan matakin na zuwa ne bayan da majalisa ta wanke tsohon shugaba Donald Trump, a shari'ar da aka yi ma sa bayan tsige shin da aka yi a karo na biyu.

An dai tuhumi Trump da ingiza magoya bayansa kai wa majalisar hari da kuma jefa rayuwar ‘yan majalisar cikin hadari.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!