Siriya:Amurka Ta Fara Gina Tashar Jiragen Sama A Kusa Da Rijiyoyin Man Fetur A Lardin Dayr-Al-Zawr

2021-02-13 20:48:35
Siriya:Amurka Ta Fara Gina Tashar Jiragen Sama A Kusa Da Rijiyoyin Man Fetur A Lardin Dayr-Al-Zawr

Gwamnatin kasar Amurka ta fara gina tashar jiragen sama a kusa da rijiyoyin man fetur da ta mamaye a lardin Dayr-Al-Zawr a arewacin kasar Siriya. Jaridar Al-Anba ta kasar Kuwai ta nakalto majiyar kungiyar ‘yan ta’adda ta SDF mai samun goyon bayan kasar Amurka ta na fadar haka a jiya Jumma’a. Kungiyar ta kara da cewa Amurka ta na gina tashar jiragen saman ne a kusa da rijiyoyin mai na Al-Omar da ke kusa da sansanin sojojin Amurka mafi girma a kasar ta Siriya.

Kafin haka dai gwamnatin Amurka ta shigo da sojojinta kasar ta Siriya ne a shekara ta 2014 da sunan yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh, ba tare da neman izinin gwamnatin kasar ba, kuma tana goyon bayan kungiyar yan ta’adda ta SDF wacce take neman bellewa da daga kasar ta Siriya don kafa kasa ta kurdawa zalla a yankin arewa maso gabacin kasar.

Banda haka gwamnatin Amurka ta sha satar danyen man fetur daga wadannan rijiyoyi man zuwa kasashen waje.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!