Ministan Tsaron Iran Ya Ce: Dukkanin Wadanda Su Ka Yi Fatan Rushewar Juyin Musulunci Sun Ci Kasa

2021-02-10 11:55:54
Ministan Tsaron Iran Ya Ce: Dukkanin Wadanda Su Ka Yi Fatan Rushewar Juyin Musulunci Sun Ci Kasa

Ministan Tsaron Iran Ya Ce: Dukkanin Wadanda Su Ka Yi Fatan Rushewar Juyin Musulunci Sun Ci Kasa

Ministan tsaron na Iran Janar Amir Hatami wanda ya ke gabatar da jawabi a daidai wannan lokacin na cin nasarar juyi, ya ce; Dukkanin wadanda suke son ganin juyin musulunci ya zo karshe, sun shiga cikin kwandon shara na tarihi, sannan kuma ya ci gaba da cewa; A halin da ake ciki a yanzu juyin musulunci ya bunkasa ya yi karfi.

Har ila yau janar Amir Hatami ya ce; Juyin musulunci ya shatawa kansa hanyar da yake tafiya akan ta, kuma cikakken ‘yanci shi ne abinda al’ummar Iran take son kai wa gare shi, don haka dole ne a yi tsayin daka da gwagwarmaya domin cimma manufa.

Bugu da kari, janar Hatami ya ce; juyin musulunci an yi shi ne ta hanyar sadaukar da rayuka, da kuma karfafa shi da jinanen wadanda su ka yi shahada wajen kare hubbarorin Ahlubayt (A.S).

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!