Iran:Manzon MDD Kan Rikicin Yemen Ya Gana Da Babban Mai Bawa Ministan Harkokin Wajen Iran Shawara
2021-02-08 09:01:04

Babban mai bawa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara kan lamuran kasa da kasa Asgar Khaji ya gana da manzon MDD na musamman a kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa jami’an biyu sun tattauna hanyoyin da za’a bi don kawo karshen yaki a kasar Yemen da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Asgar Khaji, a nashi bangaren ya bukaci a gaggauta dage takunkuman zaluncin da aka dorawa kasar ta Yemen, sannan a gaggauta kaiwa mutanen kasar kayakin agaji wadanda suka hada da abinci da magunguna.
Khaji ya ce Jumhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta taimaka a wannan bangaren, banda haka Khaji ya bayyana cewa za’a kawo karshen yaki da kuma cikekken zaman lafiya a kasar Yemen ne ta tattaunawa tsakanin dukkan yan siyasar kasar a tsakaninsu ba tare da shigar kasashen waje ba.
Tags:
manzon mdd na musamman
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!