Shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi ya jinjinawa matsayin da kasar ta dauka na mayarwa Isra’ila da martani a matsayin abin alfahari.
Raeisi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye ta gidan talabijin na kasar a daren ranar Talata yayin da yake karin haske kan bangarorin farmakin da aka kira alkawarin Gaskiya, da sojojin Iran suka kai kan Isra’ila a ranar 13 na Afrilu.
Shugaban na Iran ya nanata cewa ya kamata a tattauna wannan gagarumin aiki a tarurruka daban-daban da kuma fannonin kimiyya, bincike, siyasa da tsaro, shugaban na Iran ya ce: “wannanfarmaki abin alfahari ne na kasa kuma ana daukarsa a matsayin wani sauyi na matakan samar da daidaito a duk fadin yankin.
Raeisi ya ci gaba da cewa: wuce gona da irin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a kan ofishin jakadancin Iran a kasar Siriya ya sanya ‘yan mamaya suka yanke kauna, inda ya kara da cewa ramuwa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi wani hukunci ne day a dace.
Kafin wannan lokacin dama Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da cewa za a hukunta gwamnatin sahyoniyawa, kuma a cewar Raesi mayakanmu sun cika wannan alkawari.
Har ila yau Raeisi ya ce, wannan farmakin na jajircewa yana nuni ne a fili hadin gwiwa tsakanin bangaren soji, diflomasiyya da kafofin yada labarai