A ranar Juma’a 10 ga watan Mayu ne ake sa ran babban taron Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a kan daftarin kuduri na amincewa da baiwa Palasdinu damar zama cikakkiyar mamba a majalisar.
Wannan dai zai kasance wani ma’auni ne a duniya kan irin goyon bayan da Falasdinawa ke samu a yunkurinsu, wanda Amurka ta yi amfani da hawa kujerar naki a kwamitin sulhu a watan jiya wajen yin fatali dawannan daftarin kuduri.
Neman zama cikakken memba a Majalisar Dinkin Duniya na bukatar amincewar kwamitin tsaro mai wakilai 15 sannan kuma babban zauren majalisar.
Jami’an diflomasiyya sun ce taron na Majalisar Dinkin Duniya mai mambobi 193 na iya goyon bayan yunkurin Falasdinawa, amma har yanzu ana iya yin sauye-sauye kan daftarin bayan da wasu jami’an diflomasiyyar suka nuna damuwa game da rubutun na yanzu, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu kwafinsa, wanda ke ba da karin hakki ga .
Jaridar “Isra’ila A Yau” tana sa ran cewa mafi yawan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya za su amince da kudurin a ranar Juma’a mai zuwa, ba tare da yin amfani da hawa kujerar naki da Washington ta yi amfani da shi ba.
Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan a ranar Litinin ya yi Allah wadai da daftarin kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar a halin yanzu, yana mai cewa hakan zai bai wa Falasdinawa ‘yanci na kafa kasa.
Erdan ya ce, “Idan har aka amince da shi, ina sa ran Amurka za ta daina ba wa Majalisar Dinkin Duniya da cibiyoyinta kudade kwata-kwata kamar yadda dokokin Amurka suka tanada,” ya kara da cewa amincewa da daftarin kudurin da babban zauren majalisar zai yi ba zai sauya komai a kasa ba.