Gaza: Akalla Falastinawa 14 Sun Yi shahada A Wani Harin Isra’ila a Gabshin Rafah

Rahotanni daga yankin Rafah da ke kudancin zirin Gaza na cewa, ana ci gaba da dauki ba dadi tsakanin sojojin Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa

Rahotanni daga yankin Rafah da ke kudancin zirin Gaza na cewa, ana ci gaba da dauki ba dadi tsakanin sojojin Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a gabashin birnin.

Haka nan kuma  jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan hedikwatar karamar hukumar da ke kusa da kan iyaka da Masar da kuma gidaje, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Mayakan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas reshen Al-Qassam Brigades a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, sun kai hari kan tankar Merkava ta Isra’ila inda suka cinna mata wuta tare da kone ta kurmus.

Haka nan kuma dakarun sun kara da cewa sun yi arangama da sojojin Isra’ila da ke cikin wani gini a unguwar Shouka a Rafah.

A cikin  wata sanarwa da suka fitar, sun ce sun kai wa sojojin Isra’ila hari da makami mai linzami mai cin gajeren zango na Rajoum da kuma harsasai masu girman gaske.

An bayar da rahotanni da ke cewa akalla Falastinawa 14 yi shahada bayan kai hari kan wasu gidaje biyu da Isra’ila ta yi a gabasshin birnin Rafah, akasari wadanda suka yi shahada mata ne da kanan nan yara

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments