Search
Close this search box.

Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Kutsen Da Isra’ila Ta Yi A Rafah

Iran ta yi kakkausar suka kan kutsen da Isra’ila ta yi a birnin Rafah dake kudancin Gaza duk da gargadin da kasashen duniya suka yi

Iran ta yi kakkausar suka kan kutsen da Isra’ila ta yi a birnin Rafah dake kudancin Gaza duk da gargadin da kasashen duniya suka yi na cewa hakan zai haifar da bala’in jin kai.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kan’ani ya ce an dauki matakin ne da nufin yin zagon kasa ga kokarin da kasashen duniya ke yi na dakatar da kisan kare dangin da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza.

Wannan dai na zuwa ne bayan da sojojin Isra’ila suka kwace iko da mashigar Rafah, tare da katse wata muhimmiyar hanya ta kai agaji ga Falasdinawa kimanin miliyan 1.5 da ke mafaka a birnin da ke kan iyaka da Masar.

Jami’in diflomatsiyyan na Iran, ya ce mamayar da Isra’ila ta yi wa mashigar ya nuna irin zaluncin da gwamnatin ke yi ba tare da wani la’akari da dokokin kasa da kasa ba, wanda hakan kuma barazana ne ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

“Wannan yunkuri na gwamnatin Isra’ila an yi shi ne don mayar da kokarin kasa da kasa wajen dakatar da yaki da kuma kawo karshen kisan gillar da ake yi a Gaza,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.

Jami’in ya sake nanata cewa babban abin da ke samar da zaman lafiya da tsaro a yankin shi ne dakatar da yakin da ake yi cikin gaggawa ba tare da sharadi ba a zirin Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye.

Ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki na kasa da kasa da su matsa lamba ga gwamnatin Isra’ila ta dakatar da yakin.

Kan’ani ya ce alhakin aikata laifuka da zubar da jini a Rafah ya rataya a wuyan gwamnatin Isra’ila da kuma babbar mai goyon bayanta, wato Amurka.

“Iran ta sake yin kira ga hukumomin shari’a na kasa da kasa da su binciki laifukan cin zarafin bil adama da gwamnatin wariyar launin fata ta aikata tare da gurfanar da shugabanninta a gaban kotu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments