Shugaba, Vladimr Putin, na kasar Rasha, ya ce zai kare yanci da hurimi da tsaron kasarsa da mutuncin gwamnatinsa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da ake rantsar da shi a wani sabon wa’adin mulki.
Shugaba Putin ya fara wa’adi na biyar akan karagar mulki a wani bukin rantsar da shi a fadar Kremlin a ranar Talata, inda zai sake yin karin shekaru shida a matsayin shugaban kasar.
Tuni Putin, ya kwashe kusan shekaru 25 a kan mulki kuma shi ne wanda ya fi kowa dadewa a mulkin Fadar Kremlin bayan Josef Stalin.
Putin zai kammala wannan wa’adi a shekarar 2030, kuma bayan nan kundin tsarin mulki ya ba shi damar sake tsayawa takara da yin wani wa’adin na shekaru shida.