Iran, Ta Sanar Da Kafa Sabbin Na’urorin Tace Uranium A Tashohin Natanz Da Fordow

2021-02-04 10:06:03
Iran, Ta Sanar Da Kafa Sabbin Na’urorin Tace Uranium A Tashohin Natanz Da Fordow

Wakilin Iran, a kungiyoyin kasa da kasa dake birnin Vienna, ya sanar cewa kasar ta kafa wasu sabbin na’urorin tace sinadarin uranium a tashohin nukiliyarta na Natanz da Fordow.

Wannan dai a cewar M. Kazem Gharibabadi, wani mataki ne wanda Iran, za ta kara karfin tace sinadarin uranium dinta.

Ya ce ‘’bisa kwarewar da masananmu na nukiliya suke da ita, mun samu kafa kashi biyu na na’urorin tace sinadarin uranium samfarin IR2m su 348 wanda sun linka har sau hudu karfin IR1, wanda yanzu haka su ke aiki da UF6 cikin nasara a tashar Fordow, kuma haka yake a tashar Fordow, inda ake aikin da na’urar tace uranium samfarin UF6.

M. Gharibabadi, ya kuma ce tuni Iran, ta sanar da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya cewa da IAEA, kuma tana da hurimin ta zo ta yi bincike game da hakan.

A ranar 4 ga watan Janairu ne Iran ta sanar wa duniya cewa ta fara tace sinadarin uranium da kashi 20 cikn dari, a tashar Fordow, domin maida martani kan matakin tsohuwar gwamnatin Amurka na ficewa daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita a 2015, da kuma yi wa kasashen turai raddi game da rashin tabaka komai game da alkawuran da suka daukar mata na rage mata radadi game da jerin takunkuman da Amurka ta lafta mata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!