​Iran Ta Baiwa Ma’aikatan Jirgin Ruwan Koriya Ta Kudu Da Aka Tsare Damar Fita Daga Kasar

2021-02-03 11:38:54
​Iran Ta Baiwa Ma’aikatan Jirgin Ruwan Koriya Ta Kudu Da Aka Tsare Damar Fita Daga Kasar

Gwamnatin Iran ta baiwa ma’aikatan jirgin ruwan Koriya ta kudu damar fita daga kasar, bayan tsare su a kasar sakamakon saba ka’idar zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin tekun Fasha.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a daren jiya, inda ya bayyana cewa yanzu haka ma’aikatan jirgin ruwan na Koriya ta kudu da Iran ta tsare, sun karbi takardun izinin ficewa daga kasar ta Iran.

Ya ci gaba da cewa, Iran ta dauki matakin tsare katafaren jirgin ruwan na Koriya ta kudu ne, sakamakon saba wa ka’idar zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin tekun Fasha, da kuma rashin kiyaye wasu ka’idoji da suka shafi kare yanayi a cikin teku.

A daya bangaren mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Koriya ta kudu Mr Choi, ya gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya tare da mataimakin ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi, inda suka tattauna wanann batu, da ma sauran batutuwa da suka hada da batun sakin kudaden Iran dala biliyan 7 da Koriya ta kudu ta rike a cikin bankunanta, saboda tsoron saba wa takunkumin Amurka.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!