Iran Ta Yi Nasarar Gwada Wata Na’urar Harba Tauraren Dan Adam

2021-02-02 09:34:56
Iran Ta Yi Nasarar Gwada Wata Na’urar Harba Tauraren Dan Adam

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta sanar da yin nasarar harba wata na’urar harba tauraren dan adam data kera da kanta.

Bayan na’urar Nour-1, wannan ita ce sabuwar na’urar dake iya cilla tauraren dan adam har zuwa kilomita 500 a sararin samaniya, a cewar kakakin ma’aikatar kula da harkokin sararin samaniya ta Iran.

Iran dai na daga cikin kasashen da suka mallaki fasahar kera tauraren dan adam da cilla shi.

Ko a bara dakarun kare juyin juya halin musulinci na kasar sun yin nasarar cillawa da kuma dora wani tauraren dan adam.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!