Bayanai Na Ƙara Fitowa Dangane Da Harin Da Aka Kai Birnin Riyadh A Kwanakin Baya

Sabbin bayanai na ci gaba da fitowa dangane da harin da aka kai birnin Riyadh, babban birnin ƙasar Saudiyya a ranar Asabar ɗin da ta gabata da ke nuni da irin hasarar da harin ta haifar wa ƙasar Saudiyyan.
A
ranar Asabar ɗin da ta gabata ɗin ne dai wasu majiyoyin labarai na ƙasar Yemen
suka bayyana cewar an harba wasu makamai masu linzami daga ƙasar zuwa birnin na
Riyadh a matsayin mayar da martani da ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da
Saudiyya da ƙawayenta suke yi kan al’ummar Yemen.
Rahotannin
dai sun bayyana cewar bayan wani lokaci an ji sautin fashewar wasu abubuwa a
birnin na Riyadh, duk da cewa wasu majiyoyin labaran ƙasar Saudiyyan sun
musanta wannan labarin, to amma dai sun tabbatar da cewa an kai harin kuma makaman
kariya na ƙasar sun kakkaɓo wasu daga cikin makamai masu linzamin da aka harbo ɗin.
To
sai wasu kafafen watsa labaran yankin sun tabbatar da cewa harin an kai shi ne
kan wasu gungun gidajen gidan sarautar Saudiyya ɗin da ke birnin na Riyadh kuma
harin ya tarwatsa wajen gaba ɗaya.
Majiyoyin
labaran sun ce an kai harin ne daga ɗaya daga cikin sansanonin dakarun
gwagwarmaya na ƙasar Yemen ɗin zuwa wannan wajen mai matuƙar muhimmanci a
matsayin mayar da martani da hare-haren da Saudiyya da ƙawayen na ta suke kai wa
ƙasar ta Yemen.
Wasu majiyoyi sun ce kafafen watsa labaran Saudiyya da ƙawayenta suna ta ƙoƙari wajen ɓoye haƙiƙanin abin da ya faru ne don saboda irin hasarar da aka hasarar da harin ya haifar wa ƙasar ne.