Lebanon:Firai Ministan Riko Ya Ce Wadanda Suka Lalata Dukiyoyin Al-Umma A Tripoli Ba Zasu Tsira Daga Sakamakon Ayukansu Ba

2021-01-30 21:57:52
Lebanon:Firai Ministan Riko Ya Ce Wadanda Suka Lalata Dukiyoyin Al-Umma A Tripoli Ba Zasu Tsira Daga Sakamakon Ayukansu Ba

Firai ministan riko na kasar Lebanon Dr Hassan Diyab ya bayyana cewa wadanda suka barnata dukiyoyin al-umma a birnin Tripoli na arewacin kasar ba za su tsira daga shari’a ba.Jaridar Al-Ahad ta kasar Lebanon ta nakalto Dr diyab yana fadar haka, a yau Asabar a birnin Beirut babban birnin kasar.

Firai ministan rikon ya kuma kara da cewa zai kafa kwamiti wanda zai gudanar da bincike sosai a cikin abubuwan da suke faruwa a birnin Tripoli don hukunta wadanda suke da hannu cikin tashe tashen hankula wadanda suka yi sanadiyar raunata mutane akalla 100, daga ciki har da jami’an tsaron kasar, da kuma mutuwar mutum guda.

Wasu masana suna ganin tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma dokar hana fita wacce gwamnatin kasar ta kafa don hana yaduawar cutar korona a kasar na daga cikin dalilan da suka jawo tashe-tashen hankula, a yayinda wasu kuma suna ganin, wasu dalilai sun tabbatar da cewa akwai hannun wasu ‘yan siyasa a cikin tada rikicin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!