Amurka Na Fuskantar Barazanar Masu Adawa Da Biden

2021-01-28 21:23:33
Amurka Na Fuskantar Barazanar Masu Adawa Da Biden

Bayanai daga Amurka na cewa akwai barazanar kasar ta fuskanci hare hare daga masu tsatsauran ra’ayi dake adawa da shugabancin Joe Biden.

Wannan barazanar dai ta sanya hukumomin Amurka tsaurara matakan tsaro a cikin gida.

Ma’aikatar cikin gidan kasar ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewar ana yaudarar wasu 'yan kasar da labaran karya domin tinzira su wajen ganin sun haifar da rikici.

Gwamnatin ta ce harin da magoya bayan tsohon shugaban kasa Donald Trump suka kai Majalisar dokoki na iya karfafa wasu cigaba da kai wasu hare hare kan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati da kuma gine gine.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!