Zarif: Iran Da Armenia Za Su Ci Gaba Da Yin Aiki Tare A Dukkanin Bangarori Na Ci Gaba

Ministan harkokin wajen kasar Iran
Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, kasashen Iran da Armenia za su ci gaba da
kara bunkasa alakarsu da kuma yin aiki tare a dukkanin bangarori.
Zarif ya bayyana hakan ne yau a
lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Armenia a birnin Yerevan, a ziyarar aiki da ya fara
gudanarwa a yau a kasar ta Armenia.
Ministan harkokin wajen kasar
Iran ya ci gaba da cewa, ya yi takaici matuka dangane da rikicin da ya faru a
yankin a baya-bayan nan, domin kuwa a cewarsa duk abin da ya shafi tsaron
yankin, to ya shafi ksar Iran ne kai tsaye.
Haka nan kuma ya bayyana
matakin da gwamnatin Armenia da kuma Firayi ministan kasar suka dauka na
sulhuntawa da cewa, hakan mataki ne na jarunta, wanda ya cancanji jinjina
matuka.
Shi ma a nasa bangaren ministan
harkokin wajen kasar Armenia Ara Iwazian ya bayyana cewa, alaka tsakanin kasashen Iran da Armenia alaka ce ta
tarihi, wadda ta hada da al’adu, baya ga alaka ta kasuwanci da tattalin arziki wadda
ta hada kasashen biyu.
Zarif ya fara gudanar da ziyarar aiki ne a kasar Azerbaijan, daga nan kuma ya nufi kasar Rasha, daga can kuma zuwa Armenia, bayan nan kuma zai ziyarci kasashen Turkiya da kuma Georgia.
015