Rikici Ya Sake Ɓarkewa A Tunusiya A Daidai Lokacin Da Majalisa Ta Amince Da Kwaskwarima Ga Gwamnati

2021-01-27 13:36:29
Rikici Ya Sake Ɓarkewa A Tunusiya A Daidai Lokacin Da Majalisa Ta Amince Da Kwaskwarima Ga Gwamnati

Wani sabon rikici ya sake ɓarkewa a ƙasar Tunusiya a ci gaba da zanga-zangar da al’ummar ƙasar suke yi don nuna rashin amincewarsu da yanayin rayuwa a ƙasar bayan da ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya mutu ya mutu biyo bayan fito-na-fiton da masu zanga-zangar suka yi da ‘yan sanda a garin Sbeitla da ke wajen birnin Tunis.

Rikicin na jiya dai ya sake ɓarkewa ne bayan da gidan talabijin ɗin ƙasar ya sanar da mutuwar Haykel Rachid, ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, bayan harbinsa da bututun barkwanon tsohuwa da jami’an tsaro suka yi inda mutane suka ƙara fitowa don ci gaba da buƙatar gwamnatin ƙasar da ta yi murabus.

A jiya dai masu zanga-zangar sun mamaye majalisar ƙasar a ƙoƙarin da suke yi na neman sauyi a ƙasar wanda suka ce sama da shekaru goma da ƙoƙarin da suka yi na neman sauyi a ƙasar amma dai ba su cimma burinsu ba.

To sai dai a ɓangare guda kuma majalisar ƙasar ta amince da yin kwaskwarima ga gwamnatin ƙasar wanda ake ganin hakan zai ƙara rikicin da ke tsakanin shugaban ƙasar da kuma firayi ministansa.

Tun da fari dai firayi ministan ƙasar Hichem Mechini ya gabatar da sunayen sabbin ministocin gwamnatinsa wanda ya ce yana fatan hakan zai sanya sabon jini cikin gwamnatin, lamarin da shugaban ƙasar Kais Saied ya ce ba zai amince da shi ba don kuwa hakan babu abin da zai haifar in banda ƙarin rarrabuwan kai a tsakanin al’ummar ƙasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!