​Amurka: Waɗanda Suka Kamu Da Cutar COVID-19 Sun Haura Mutum Miliyan 25

2021-01-25 17:41:44
​Amurka: Waɗanda Suka Kamu Da Cutar COVID-19 Sun Haura Mutum Miliyan 25

Amurka ta tabbatar da cewa sama da mutane miliyan 25 ne suka kamu da cutar COVID-19 (Coronavirus) a ƙasar a daidai lokacin da sabon shugaban ma’aikatar fadar White House na Amurkan ya zargi gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da gazawa wajen samar da rigakafin cutar da ake buƙata.

Wannan bayani na adadin waɗanda suka kamun yana cikin wata ƙididdiga ce da Jami’ar John Hopkins ta Amurkan ta fitar kan yanayin yaɗuwar cutar a Amurkan inda ta ce adadin waɗanda suka kamu a Amurkan ya kai mutane miliyan 25 wanda yake a matsayin kashi 1 cikin huɗu na adadin dukkanin waɗanda suka kamu a duk faɗin duniya.

A wata hira da yayi da tashar talabijin ɗin NBC ta Amurkan, shugaban Ma’aikatan fadar White House ɗin Ron Klain gwamnatin da ta gabatan ta yi riƙon sakainar kashi ga batun rarraba rigakafin cutar a ƙasar duk kuwa da irin yadda cutar take yaɗuwa a watannin ƙarshe-ƙarshe na gwamnatin.

Sabuwar gwamnatin Biden ɗin dai tana fatan za ta daƙile yaɗuwar cutar ta hanyar rigakafin da za ta raba a ƙasar sai dai kuma wasu rahotanni suna nuni da cewa akwai kwangaba-kwanbaya cikin yadda ake raba rigakafin inda a wasu wajejen ma ake fuskantar ƙarancinsu.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!