Najeriya: Kotu Ta Amince Da Cewa Mai Dakin Sheikh Zakazaky Na Dauke Da Cutar Korona

Kotu a jihar Kaduna ta amince da
sakamakon gwajin cutar corona da ke tabbatar da cewa, maid akin Sheikh Ibrahim
Zakzaky Malama Zeenat Ibrahim tana dauke da cutar.
Tashar Channelstv ta bayar da
rahoton cewa, kotu ta bayar da umarni ga jami’an da ke kula da gidan kason Kaduna,
da su dauki Malama Zeenat Ibrahim zuwa wurin da ake killace jama’a da suke
dauke da cutar domin bata kula ta musamman.
Tun a ranar Alhamis da ta gabata, a
wata zantawa da ya yi da tashar talabijin ta Channels tv, shugaban dandalin
yada labarai na Harka Islamiyya Malam Ibrahim Musa ya yi bayani kan sakamakon
gwajin da aka yi wa Malama Zeenat Ibrahim, wanda ke tabbatar da cewa tan adauke
da cutar.
Sai dai jami’an gidan kason na
Kaduna tun daga lokacin fitar da sakamakon suka karyata hakan, inda suka
bayyana rashin amincewarsu da sahihancin sakamakon gwajin, amma yanzu bayan umarnin
da kotu ta bayar, sun amince da sakamakon gwajin.
Kafin wanann lokacin Muhammad
Ibrahim Zakzaky dan Sheikh Ibrahim Zakzaky ne ya fara fitar da sanarwa, kan
cewa mahaifiyarsa da ke tsare tana fama da cutar corona a cikin gidan kaso.
015