MDD : Yarjejeniyar Haramta Makamman Nukiliya Ta Fara Aiki

2021-01-22 16:11:41
MDD : Yarjejeniyar Haramta Makamman Nukiliya Ta Fara Aiki

A wannan Juma'ar ce yarjejeniyar haramta amfani da makamman nukiliya ke fara aiki.

Yarjejeniyar ta tanadi daina yin bincike da yin gwaje-gwaje da kuma barazanar amfani da makaman nukiliya.

Wannan dai wani buri ne da MDD, ta jima tana yunkurin cimmawa tsakanin kasashen duniya.

Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya bayyana lamarin a matsayin babban mataki da aka dauka na cimma burin dakatar da kera makaman nukiliya.

Saidai kash, kasashen da suka mallaki makaman nukiliyar ba sa cikin wadanda suka sanya hannu a yarjejeniyar.

Kasashe goma da suka mallaki makamman nukiliya, sun hada Amurka, Rasha, China, Faransa, Biritaniya, Indiya, Pakistan, da Koriya ta Arewa, sai kuma Isra’ila, duk da cewa ita kam a hukumance bata amince cewa tana da makamman nukiliyar ba.

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, wacce duniya ke ta takaddama kan shirin nukiliyarta, na daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!