Aƙalla Mutane 28 Sun Mutu Biyo Bayan Wani Harin Ƙunar Baƙin Wake A Birnin Bagadaza, Iraƙi

2021-01-21 20:59:02
Aƙalla Mutane 28 Sun Mutu Biyo Bayan Wani Harin Ƙunar Baƙin Wake A Birnin Bagadaza, Iraƙi

Rundunar sojin ƙasar Iraƙi ta bayyana cewar alal aƙalla mutane 28 sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kunar baƙin wake da aka kai wani titi da ake hada-hadar kasuwanci a babban birnin ƙasar Iraƙin, Bagadaza, wasu rahotanni suna cewa akwai yiyuwar adadin ma ya ƙaru.

Yayin da yake magana kan hakan, daraktan tabbatar da tsaron birnin na Bagadaza, Birgediya Janar Hazem al-Azzawi, ya shaida wa Kamfanin dillancin labaran Iraƙin (INA) cewa wasu tagwayen fashewa sun faru a kasuwar Bab al-Sharji da ke cike da jama’a a yau ɗin nan Alhamis bayan watanni na zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Jami’in ya ci gaba da cewa tagwayen fashewar sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 28 da kuma raunana wasu 73 na daban.

Har ila yau kamfanin dillancin labaran AFP ya jiyo wasu majiyoyin asibiti suna cewa akwai yiyuwar adadin waɗanda suka mutu ko kuma suka samu raunukan ya ƙaru saboda munin lamarin suna masu cewa tuni ma’aikatar lafiya ta buƙaci cibiyoyi lafiya da ba da agaji da su kai wa waɗanda lamarin ya shafa ɗauki.

Kakakin sojin Iraƙin, Yahya Rasool ya ce wasu ‘yan ƙunar baƙin wake su biyu ne suka tayar da bama-baman da suka yi jigida da su a lokacin da jami’an tsaro suke binsu da nufin kama su.

Har yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗau alhakin wannan harin, duk da cewa mafiya yawan irin waɗannan hare-haren ƙungiyar ta’addancin nan ta ISIS ce take kai su a Iraƙin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!