​Zarif, Ya Yi Maraba Da Tayin Qatar Na Neman Sansanta Iran Da Kasashen yankin tekun Fasha

2021-01-20 14:57:07
​Zarif, Ya Yi Maraba Da Tayin Qatar Na Neman Sansanta Iran Da Kasashen yankin tekun Fasha

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya yi maraba da matakin kasar Qatar ne neman sassanta kasarsa da kasashen Larabawa na tekun fasha.

A jiya ne dai Qatar, ta bakin ministan harkokin wajenta, Mohammed ben Abdulrahman ben Jassim Al Thani, ya ce a shirye kasarsa ta ke ta gudanar da wata tattaunawa ta tsakanin Iran da kasashen larabawa.

Iran ta ce daman hakan yana cikin fatan da takeyi na samun fahimtar juna domin samar da zaman lafiya da tsaro da ci gaba a yankin dama duniya baki daya.

Qatar dai ta ce fatan hakan ya samu tsakanin kasashen yankin, kamar yadda su ma wasu kasashen yankin na teklun fasha ke fatan hakan.

Iran da Qatar da na dadadiiyar alaka ta zamantakewa, saidai an bayyana alakar ta fadada sosai a cikin ‘yan shekarun baya baya nan, saboda yanke alaka da Saudiyya da kawayenta sukayi da Qatar din a cikin shekarar 2017, saidai daga bisanin nan sun sassanta.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!