Rahoto: Mutane 348 Aka Kashe, 411 Aka Sace A Watan Disamban 2020 A Duk Faɗin Nijeriya

2021-01-19 20:21:23
Rahoto: Mutane 348 Aka Kashe, 411 Aka  Sace A Watan  Disamban 2020 A Duk Faɗin Nijeriya

Alal aƙalla mutane 348 aka kashe sannan wasu 411 kuma aka sace su a duk faɗin Nijeriya a watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2020 a ci gaba da rikice-rikice da tashin hankalin na rashin tsaro da ke faruwa a ƙasar.

Kafar watsa labaran Premium Times ta Nijeriya ta bayyana cewar wannan bayani yana cikin wani rahoto ne da wata ƙungiya mai suna Nigeria Mourns ta fitar inda ta ce ta tattaro wannan bayanin ne daga labaran da ta tattaro daga jaridu da kuma majiyoyin iyalan da aka kashe ɗin tsawon wannan lokacin.

Rahoton ya ce bayanan da suka tattaro din sun shafi jihohi 27 na ƙasar inda ya ce daga cikin mutane 348 ɗin da aka kashe a watan, 315 daga cikinsu fararen hula ne alhali 33 kuma daga cikinsu jami’an tsaro ne.

Har ila yau rahoton ya ce kimanin mutane 411 ne aka sace a duk faɗin Nijeriyan a watan Disamban shekarar da ta gabatan.

Rahoton ya ce jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Nijeriyan da ke fuskantar matsalar Boko Haram ita ce kan gaban wajen yawan mutanen da suka rasa rayukan na su, inda ya ce kimanin mutane 70 ne aka kashe a watan.

Nijeriya ɗin dai tana fuskantar matsalar rashin tsaro cikin shekarun baya-bayan nan da suka haɗa da hare-haren ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da kuma masu ɗauke da makami masu satar mutane bugu da ƙari kan rikice-rikice na kabilanci da sauransu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!