Iran : Ba Wani Abu Da Ya Fi Kwato ‘Yancin Masallacin Qods A Yanzu

2021-01-19 09:38:53
Iran : Ba Wani Abu Da Ya Fi Kwato ‘Yancin Masallacin Qods A Yanzu

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa babu wani abu da ya fi muhimmaci ga musulmi a wannan karni na 21, kamar kwato ‘yancin masallacin Qods.Wannan kalamman sun fito ne a ta bakin shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran, Mohammad-Baqer Qalibaf.

Ya ce Amurka, da mahukuntan yahudawan mamaya na Isra’ila, babban burin da suka sanya a gaba shi ne su fitar da kasashen musulmin yankin daga duk wata magana data shafi birnin Qods, ya zama kawai na yahudu.

M. Qalibaf, ya bayyana hakan ne yayin wani taron karfar bidiyo da ya gudana jiya Litini a Tehran, kan batun Falasdinawa, wanda ya samu halartar masana daga kasashen musulmi da dama.Iran, ta bakin shugaban majalisar dokokin kasar ta bukaci kasashen musulmi da kada su yarda da yunkurin raba kanuwansu game da kwatar wa da Falasdinwa yancinsu da kuma kare masallacin Qods.


Babban abun damuwa ma a cewarsa, shi ne yadda wasu kasashen musulmin da kungiyoyin kasa da kasa irinsu MDD, da hukumar kare hakkin dan adam sukayi gum da bakinsu kan irin muggan laifukan da Isra’ila ke aikatawa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!