Amurka : Ana Zaman Dar-dar Gabanin Rantsar Da Biden

2021-01-18 14:57:19
Amurka : Ana Zaman Dar-dar Gabanin Rantsar Da Biden

Rahotonni daga Amurka na cewa ana zaman dar-dar a Washington, gabanin bikin rantsar da zababen shugaban kasar Joe Biden a ranar 20 ga watan nan.

Ko a makon jiya hukumar binciken manyan laifuka ta kasar FBI, ta bankado wani shirin da gungun masu zafin ra’ayin goyon shugaba Trump mai barin gado ke yi, na kokarin tayar da hargitsi ta hanyar zanga-zanga kafin rantsar da sabon shugaba Joe Biden.

Wani abu da ya tayar da hankali kuma shi ne yadda jami’an tsaron kasar suka kame wani mutum dauke da tarin makamai da albururai yayin da yayi kokarin wuce wani shingen bincike a birnin Washington, a gaf da zauren majalisar dattijan kasar, inda ake sa ran rantsar da zababben shugaban kasar a ranar Laraba.

Yanzu haka dai hukumomin tsaro sun tsaurara matakan tsaro a daukacin Amurka ciki har da birnin Washington, a wani al’amari da ba’a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!