Rahotanni da cibiyoyin gwamnati a gaza sun yi ishara game da irin taadanci da sojojin isra’ila suka yi a Asibitin Nasir ciki har da yadda suka yi gunduwa gunduwa da jikin falasdinawa tare da sace wasu sassan jikinsu,
Har ila yau sun kara da cewa daga cikin mummunan laifin da suka tafka akwai bizne falasdinawa da dama acikin kabarin gama gari da ransu, yanzu haka dai a na ci gaba da bincike don gano wasu gawawwakin da aka bizne
Hukumar bada kariya ga alumma a yankin Gaza ta kafa wani kwamiti na kasa da kasa don gudanar da bincike kan taadanci da Isra’ila ta tafka a Gaza na haka manya-manyan ramuka da kuma boye gawawwakin shahidai da aka yi gunduwa gunduwa da su ,
Ya zuwa yanzu an gano gawawwakin falasdinawa 392 da aka bizne a kabarin gama – gari a Asibitin nasir wanda kashi 58 cikin dari ba’a iya ganesu ba.