Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya fadi cewa jinane masu tsarki na shahidan harin Isra’ila a ofishin jakadancin Iran dake Siriya ya jawo daukaka ga kungiyoyin yan gwagwarmaya da kuma kaskantar da gwamnatin yahudawan sahuniya a duniya.
Da yake bayani game da martani da dakarun kare juyin musulunci suka mayar ga ta’ddancin Isra’ila yace daga karshe albarkacin jinan shahidai zai kai ga kawo karshen gwamnatin sahyuniya da Taadancin da take tafkawa kan falasdinawa.
A farkon watan Aprilu ne gwamnatin israila ta kaddamar da hali kan ofishin jakadancin iran a Damaskas na kasar siriya, da yayi sanadiyar shahadar 7 daga cikin masu bada shawara ga tsarin musulunci na kasar iran.