Uganda : Bobi Wine Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe

2021-01-17 09:14:51
Uganda : Bobi Wine Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zabe

Jagoran ƴan adawar Uganda Robert Kyagulanyi, da akafi sani da Bobi Wine ya yi wasti da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar Alhamis, da hukumar zaben kasar ta sanar a jiya, inda ta bayyana shugaba mai ci Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben.

Bobi Wine da sauran yan takaran da suka shiga zaben sun yi zargin tafka magudi.

A sakamakon zaben, Museveni ya samu kashi 58.64% na kuri'un da aka kada yayin da babban abokin hammayassa Bobi Wine ya samu kashi 34.83%.

Kafin hakan dama Jagoran ‘yan adawan na Uganda ya nuna damuwa akan yadda sojoji suka yiwa gidansa kawanya gabanin fitar da sakamakon zaben.

M Bobi Wine, ya kuma koka kan cin zarafin magoya bayansa da jami’an tsaro suka yi, da kuma hana wa magoya bayansa sayan ido a zaben.

Shugaba Museveni mai shekaru 76 ya shafe shekaru 34 yana mulkin kasar, wanda a yanzu kuma zai mulki kasar na wani wa’adin mulki karo na shida, idan kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da nasararsa a wannan zaben.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!