Iran: Rundunar Sojin Ruwa Ta Fara Gudanar Da Wani Gagarumin Atisayi A Cikin Tekun Oman Da Tekun India

Rundunar sojojin ruwa ta kasar Iran
ta fara gudanar da wani gagarumin atisayi a yau a cikin tekun Oman da kuma
tekun India.
Mai magana da yawun rundunar sojin
ruwa ta kasar Iran Admiral Amir Hamza Ali Kaviyani ya fadi cewa, an fara
gudanar da wannan atisayi ne a yau, kuma za a gwada wasu manyan makamai masu
linzami da Iran din ta kera, wadanda ake harba su daga cikin teku zuwa doron
kasa.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, akwai
makamai masu linzami da jiragen ruwa masu tafiya karkashin ruwa suke harbawa
domin nutsar da manyan jiragen ruwa na yaki da ke tafiya a kan doron ruwa, wanda su za a gwada wasu daga
cikinsu a wannan atisayi.
Admiral Hamza Ali ya ce, babbar
manufar gudanar da wannan atisayin ita ce kara zama cikin shirin ko ta kwana,
domin fuskantar kowace irin barazana daga makiyan kasar, inda ya ce sun shirya
tsaf domin mayar da martani da ya dace da kowace irin tsokana.
Baya ga haka kuma ya ra da cewa,
wannan atisayin ya kara tabbatar da cewa, kasashen yankin za su iya tabbatar da
tsaro a cikin yankin gabas ta tsakiya da kansu, ba sai wasu sun yi musu shigar
shugula ba.
A yau ne rundunar sojin ruwan Iran
ta karbi katafaren jirgin ruwan yakin samfurun MAKRAN, wanda yake daukar
jiragen sama na yaki da kuma dubban sojoji mayaka, gami da motocin yaki masu sulke
da tankoki, wanda kuma zai harba manyan makamai masu linzami daga cikin ruwa zuwa doron kasa.
Katafaren jirgin ruwan na MAKRAN dai kasar Iran ce ta kera shi, wanda kuma a halin yanzu tana mallakar guda hudu irinsa.
015