Libya: An Tattauna Tsakanin Yan Siyasar Kasar Libya Dangane Da Kasafin Kudi

2021-01-13 14:35:30
Libya: An Tattauna Tsakanin Yan Siyasar Kasar Libya Dangane Da Kasafin Kudi

Jami’in gwamnatoci biyu na kasar Libya sun gana a tsakaninsu a jiya don tattauna batun kasafin kudin kasar. Tashar talabijin ta Skynews al-arabi ta nakalto ma’aikatar kudi na gwamnatin Tripoli tana cewa wasu jami’anta da na gwamnatin gabacin kasar sun hadu a garin “Al-Burka”inda suka tattauna yadda zasu hadi kasafin kudin gwamnatocin biyu na wannan shekarar.

Hade kasafin kudin gwamnatocin biyu na wannan shekara ta 2021 dai zai bawi gwamnatocin biyu aike tare da gudanar da zabubbukan majalisar dokokin hadin kan kasa da kuma gwamnatin hadin kan kasa a cikin watan Disamba na wannan shekara.


019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!