Gwamnatin Kasar Iraki Ta Kammala Shirye-Shiryen Gudanar Da Zaben ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar

2021-01-13 08:56:11
Gwamnatin Kasar Iraki Ta Kammala Shirye-Shiryen Gudanar Da Zaben ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar

Shuwagabannin gwamnati da na bangaren sharia da zartarwa na kasar Iraki sun bada sanarwar kammala shirye-shirye na gudanar da zaben majalisar dokokin kasar.

Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ya nakaltou jami’an gwamnatin kasar ta Iraki suna cewa a shirye suke don gudanar da zaben yan majal;isar dokoki a cikin watan Yuni mai zuwa.

A jiya Talata ce shugaban kasar ta Iraki Barham Saleh ya bayyanawa, gamayyar jam’iyyun kurdawa ta Amal na kasar kan cewa zabe mai inganci shi ne zai iya kawo gyara a kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!