Twitter Ya Dakatar Da Shafukan Magoya Bayan Trump 70,000

2021-01-12 21:23:48
Twitter Ya Dakatar Da Shafukan Magoya Bayan Trump 70,000

Shafin sada zumunta na twitter, ya sanar da dakatar da shafuka 70,000 dake da alaka da gungun magoya shugaba mai barin gado na Amurka, Donald Trump.

Twitter, ya ce ya dakatar da shafukan ne domin kaucewa yin amfani dasu domin tayar da irin boren da ya faru a makon da ya gabata a birnin Washington.

An dai fara toshe shafukan ne tun bayan da aka dakatar da shafin shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, bayan da magoya bayansa suka suka kutsa a cikin ginin majalisar dokokin kasar da nufin hana muhawarar da ake ta tabbatar da nasarar Joe Biden a hukumance a matsayin zababben shugaban kasar.

Wata sanarwa da shafin twitter, ya fitar ta ce shafukan na yada bayanai masu hadari, a daidai lokacin da ake tunkarar bikin rantsar da zababen shugaban kasar Joe Biden a ranar 20 ga watan nan.

Rahotanni daga AMurkar na cewa akwai yiwuwar magoya bayan Trump, su tayar da hargitsi gabanin bikin.

Kutsen da magoya bayan Trump, sukayi a ranar Laraba data gabata, a majalisar dokokin kasar ya dai zubar da kimar Amurka a idon duniya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!