Iyalan Masanan Nukiliyan Iran Da Aka Kashe Sun Kai Karar Amurka Saboda Goyon Bayan Ayyukan Ta’addancin Isra’ila

2021-01-12 09:16:10
Iyalan Masanan Nukiliyan Iran Da Aka Kashe Sun Kai Karar Amurka Saboda Goyon Bayan Ayyukan Ta’addancin Isra’ila

Iyalan masanan nukiliyan Iran da aka kashe sun shigar da ƙarar Amurka saboda goyon bayan da take ba wa haramtacciyar ƙasar Isra’ila cikin wannan ɗanyen aiki nata a kan al’ummar Iran.

Lauyan iyalan masanan nukiliyan, Somayeh Afzali Niku ce ta bayyana hakan a wata tatttaunawa da ta yi da tashar talabijin ɗin nan ta Press TV da ke watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran tana mai cewa sun ɗau wannan matakin ne don tabbatar wa duniya cewa wannan ɗanyen aikin na kashe masanan ba zai tafi haka kawai ba.

Lauyan ta ƙara da cewa wajibi ne a hukunta dukkanin waɗanda suke da hannu cikin wannan ɗanyen aikin ciki kuwa har da wasu shugabannin Amurkan da jami’an ƙasar musamman sakatarorin harkokin waje da na baitul mali.

Lauyan wacce tace ƙara ta ƙumshi mutane da dama, tana magana ne kan neman biyan diyyar na irin hasarar da wannan kisan gillan ya haifar wa iyalan mamatan wanda kuma za ta buƙaci a ƙwace kaddarorin Amurkan da suke yankin nan.

Cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan dai an kashe wasu masana harkokin nukiliya na Iran da ake zargin ‘Isra’ila’ da hannu cikin hakan, na baya-bayan nan shi ne kisan gillan da aka yi wa Dr. Muhsin Fakhrizadeh wanda Iran ɗin ta ce ko shakka babu za ta ɗau fansar jinin waɗannan gwaraza nata da aka zubar ko ba daɗe ko ba jima.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!